SHARHIN NA MUSAMMAN KAN FIM DIN MALIKA.

Sharhi kan fim xin Malika 1 da na 2
Kamfanin: Saira Movies.
Labari/Tsarawa: Maje El-hajij.
Manajan shiri: Sani Mai iya.
Shiryawa: Nazifi Asnanic.
Ba da Umarni: Aminu Saira.
Shekarar fitowa: Disamba, 2011
Lokaci Malika 1: Awa 1 da minti 13 da kuma sakwan 45
Lokaci Malika 2: Awa 1 da minti 13 da sakwan 13
Yawan fitowa Malika 1: 32
Yawan Fitowa Malika 2: 26
‘Yan wasa:
Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi, Maryam Muh’d, Rabi’u Rikadawa, Jamila Umar, Sadiq Ahmad, Hafsat Sharaxa da sauransu.
Labarin Abdulmajid (Ali Nuhu), wani xan jarida mai yin aiki tsakaninsa da Allah ne da matarsa Karima (Nafisa Abdullahi), mai tsananin kishi da zurfin ciki, wanda Malika (Maryam Muh’d), mace marar kamun kai, kuma tsohuwar budurwar Abdulmajid, suka haxa kai da qanwarsa Ummi (Jamila Umar) da mijinta Alhaji Barmo (Sadiq Ahmad), wajen kunna masa wutar rikici da rashin zaman lafiya a gidansa, sakamakon rubutu da yake yi a kan Alhaji Barmo, saboda zaluncin da yake yi, rashin zaman lafiyar da har ya shafi gidan surukansa, domin Malika ta kuma yi soyayya da Alhaji Bukar (Rabi’u Rikadawa) wanda suruki ne kuma mai kamfanin jaridar da Abdulmajid yake aiki.
Darasi
Bai kamata mata tana voye wa mijinta wani abu ba, ko riqa fushi da shi, hakan zai rura wutar rikici a tsakaninsu. Yana da kyau xan jarida ya yi aikinsa tsakani da Allah, haka zai sanya a samu adalci a tsakanin al’umma, sannan bai kamata mutum ya yi tarayyar da macen da ba ta da tarbiyya ba, da dai sauransu.

Tsaruwa
Fim xin Malika, ya tsaru, domin a waxansu fina-finai akan iya hasashen mai zai faru a fim, amma a fim xin Malika ba wanda ya isa ya gane mai zai faru a gaba.
Gwanintar Harshe
An gina fim xin bisa qwarancewar gwalon-gwason furta bayanai, misali a xauka ta 17 (Kashi na xaya), zantuttukann da suka gudana tsakanin Ummi da Karima; Misali, abin da kamar wuya kixan ganga da lauje. Ba a kama zomo daga zaune. Ban ga ta zama wai an sace xan biri. A fitowa ta 19 (kashi na xaya), Karima ta ce da Malika, tsangayar kura ba a bai wa kare dillanci, sama ta yi yaro nisa sai dai ya tada kai ya yi kallo, kifi da kaska ba sa zama a waje xaya. Haka a fitowa ta 7 da ta 9 da kuma ta 17 (duka a kashi na xaya). Haka a kashi na biyu, an nuna gwanintar harshe a fitowa ta 12 da ta 14 da ta 15 da ta 21, a takaice duk yawancin fitowar an nuna gwanintar harshe.
Kirari da maganar azanci
An qawata fim xin da kirari, misali a fitowa ta 17 (Kashi na xaya), an yi wa Malika kirari da: Malika cillakowa mai ci ranin lalata, idan ba ta lalata miki aure ba, za ta lalata miki miji; Malika qafar ungulu vata miya ce, sai ta kashe miki aure, ta kuma qi auren mijinki……
A fitowa ta 15 (kashi na xaya) an samu azanci, misali lokacin yaqin cacar baki tsakanin Alhaji Barmo da Abdulmajid, inda Abdulmajid ya ce, Hargagin damisa baya razana ‘ya’yan zakanya, atishawar quda ba ta fasa tulu. Haka a fitowa ta 9 da ta 10 da ta 19 duka a kashi na xaya. Haka a kashi na biyu, a fitowa ta 22 da ta 14 da dai sauransu.
Kura-kurai:
Nahawu
A rubutun Turanci:
A jikin kwalin fim xin an rubuta; The Dream of Nazifi Asnanic, wanda hakan ba shi da wani amfani. Haka an rubuta Story/Screenplay da A film by Aminu Saira da Marketed & Distributed, maimakon Labari/Tsarawa da Fim xin Aminu Saira da Kasuwanci da Dillanci. Idan ma sai an yi rubutu da Turanci sai a yi kamar haka: Labari/Tsarawa, sannan sai a rubuta a cikin baka-biyu (Story/Tsarawa) ko kuma a rubuta a qarqashin Labari/Tsarawa.
A rubutun Hausa:
Yayin rubuta godiya ta musamman, an rubuta Zangin Banta Hotel Zanfara, maimakon Zamfara, Junaidu Danfulani maimakon Xanfulani. Haka an rubuta, waka da hada hoto da rera waka da kida, maimakon waqa da rera waqa da kixa.
A furucin baka:
An samu kura-kurai ya yin furta waxansu jimloli, misali, a fitowa ta 13 (kashi na xaya), lokacin da Kaka (Hafsat Sharaxa) da Malika suke zance, lokaci da Malika za ta ce: wata gaskiya maimakon wacce gaskiya. Ungule ne za ta koma gidanta na tsamiya, maimakon ungule ce. Indan ta wannan ne, kwananan za ki fara guxan xaurin aure, maimakon guxar xaurin aure. Matan mutum kabarinsa, maimakon matar mutum kabarinsa. Haka a lokaci da Kaka za ta ce: Ina da damuwa da ya fi, maimakon damuwar da ta fi. Yanzu ba a kan qin gaskiyanki ba, maimakon qin gaskiyarki.
A fitowa ta 15 (kashi na xaya); lokacin da Alhaji Barmo ya iske Abdulmajid a wajen cin abinci, Alhaji Barmo, ya ce, sallama bishara ne, maimakon bishara ce. Haka a fitowa ta 27 (kashi na xaya); lokacin da Malika ta je gidan Abdulmajid, domin kai wa togaciyar Karima, ta ce, Karima ne ta je har gida, ta ce na sace mata xa, maimakon Karima ce ta je har gida ta ce na sace mata ‘ya. A fitowa ta 32 (kashi na xaya), Malika ta ce, bari na baki lambar wayana ko? Maimakon bari na ba ki lambar wayata ko? Da dai sauransu.
An samu kura-kurai na shigar iska ko kuma wata baquwar qara, yayin xaukar waxansu fitowa, waxanda suka haxa da fitowa ta 3 da fitowa ta 12 da fitowa ta 14 (duka a kashi na xaya). A fitowa ta 2 da ta 9 (kashi na biyu) kyamara ta yi rawa. A fitowa ta 6 (kashi na xaya); Ummi (Jamila Umar), ta kalli darakta ko wani ma’aikacin shirin fim a lokacin da ta naxe sallaya za ta fita daga xaki.
Wani abu kuma, a fitowa ta 30 (kashi na xaya), shi ne, ya za a yi a ce Alhaji Bukar ya kawo Malika gidan kakarta, kuma Abdulmajid da Karima suna qofar gidan, har sun ma fito a cikin mota, amma a ce Malika da Alhaji Bukar ba su gan su ba.
Haka a qarshen fim xin, lokacin da ake rubuta sunayen ma’aikatan fim, sunayen ba su fita sosai ba. Kazalika, bai kamata Alhaji Bukar a matsayinsa na surukin Abdulmajid, sannan ya vare baki yana shaida masa, irin yadda son Malika ya yi masa kamun-kazar ququ ba, kamar yadda ya yi a fitowa ta 13 (kashi na biyu) ba, domin hakan ba al’adar Bahaushe ba ce.
Shawara
A gaskiya ya dace a ce an yi tarjamar fim xin zuwa turanci ko faransanci kodai zuwa wani yare (Subtitle), don ya taimaki masu kallo da ba Hausawa ba. ANGAISHE DA Bashir Musa Liman.

Comments

Popular posts from this blog

Sarkin Jama’are ya albarkaci wakata - Badariyya meke tsakaninta da AMINU BAGWAI HAR YAYI MATA WAKA?

Lalacewar mata a Nijeriya

Zango Ya sayawa Matarsa Dankareriyar Mota